Assalamu Alaiki Ya Zahra
Barka da zuwa shafin Nana
Wacece Sayyidah Fatimah Az-Zahra (a.s) ?



Gurin Haihuwarta: Garin Makka mai Alfarma.










Firdausi Bashir Mansir
MAKASUDIN WANNAN SHAFI
Na bude wannan shafi ne domin isar da wani haske game da rayuwa, karantarwa da kuma tarbiyyar sayyidah Fatimah (a.s) a cikin harshen Hausa domin amfanin 'yan'uwa mata da sauran al'umar annabi. Ina mai fatan samun tubarrakin Sayyidah Fatimah (a.s.) da Iyalanta tsarkaka.(a.s.)
Nana Firdausi Bashir (Editar shafi)
Allahumma Swalli ala Muhammad wa ali Muhammad
________________________ An haifi Fatima al-Zahra (a.s) ne a ranar juma'a, Ashirin ga watan Jimada Sani, shekaru biyar bayan aiko Annabi. Bayan haihuwar Manzon Allah (s.a.w.a) ya amshi 'yarsa da farin ciki da amincewa, ya kuma sa mata suna Fatima.
An haifeta kuma ta tashi a gidan Annabci, ta tarbiyyantu a inuwar wahayi, ta kuma sha kaunar imani da kyawawan dabi'u daga Khadija.
Fatima ta kasance mai dauke da ruhin Manzon Allah (s.a.w.a) da dabi'unsa, don haka ta zama mai gado da kuma tsananin kama da shi, har ma A'isha ta taba cewa:
"Ban ga wanda ya fi kama da Manzon Allah (s.a.w.a) a rashin magana da kyauta fiye da Fatima 'yar Manzon Allah ba, a tsayuwarta da zamanta. Ta kasance idan ta shiga wajen Annabi (s.a.w.a) ya kan mike ya tarbe ta, ya zaunar da ita a wurin zamansa. Haka nan idan Annabi ya shiga gare ta, ta kan mike daga wajen zamanta ta tarbe shi, ta zaunar da shi a wajen zamanta(1)"
Allah Ya so Fatima ta fara yarintarta a wani yanayi mafi tsananin wahala da kuntatawa daga matakan da'awar Musulunci; kuma wanda mahaifanta suka fi shan wahala da cutuwa a cikinsa. Ga dai Kuraishawa nan na tilasta takunkumi tattalin arziki a kan Manzon Allah da danginsa daga banu Hashim da mayar da su saniyar-ware. A wannan lokacin ne aka tsare Manzon Allah (s.a.w.a) a Shi'abi Abi Talib tare da matarsa Khadija, 'yarsa Fatima da sauran musulmi.
Shekarun takunkumi sun wuce tare da matsanancin hali, har zuwa lokacin da Manzo (s.a.w.a) ya fita daga cikinsa tare da wadanda ke tare da shi alhali Allah Ya rubuta masa nasara da galaba. Khadija kuwa ta fita daga cikin shi alhali shekarun sun yi mata nauyi, gajiyar takunkumi da matsalolinsa sun raunana ta. Wannan ya sa ajalinta ya gabato.
Allah Ya zabar mata makwabtakarSa, inda ta rasu a wannan shekara, bayan 'yan watanni kuma sai Abu Dalib baffan Annabi (s.a.w.a), mai kariya da taimakon Musulunci; wanda Manzo (s.a.w.a) ya bayyana yadda ya yi rashinsa da fadarsa cewa: "Kuraishawa ba su fara matsamin ba har sai da Abu Dalib ya yi wafati(2)",ya rasu.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi bakin ciki kuma ya ji kadaici a saboda rabuwa da Khadija. Domin ya yi rashin Khadija matarsa, masoyiyarsa kuma mai taimakonsa. Kamar yadda ya yi rashin baffansa mai kariya gare shi; don haka ya kira wannan shekara da sunan Shekarar Bakin-Ciki.
Fatima, karamar 'yar Manzo (a wannan lokaci) ma ta rayu cikin wani bangare na wannan bakin ciki, ita ma ta yi makoki, don kuwa ita ma bala'in wannan shekarar ya taba ta; yayin da ta rasa uwa mai tausayi; alhali kafin nan ta koshi da kaunarta da lurarta, don haka (yanzu) ta lullubu da bakin-ciki da maraici.
Sanannen abu ne cewa dole ne wannan rasuwa ta girgiza Fatima don kuwa ta rasa mahaifiyarta, ta rabu da cibiyar kaunarta, don haka sai dacin rabuwa ya cika zuciyarta ya kuma girgiza ta.
Babanta Manzon Allah (s.a.w.a) ya dandana bakin-cikin Fatima; yayin da ya ga karamar 'yarsa na zubar da hawayen rabuwa, sai zuciyarsa mai tausayi ta yi kuna, jiyayyar nan tasa ta uba mai kauna ta gaskiya ta tabu, don haka sai ya kusanci Fatima don ya musanya mata abin da ta yi rashi na kauna da kusanci da kaunarsa da taushin zuciyarsa.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a) ya so Fatima kuma ita ma ta so shi; ya tausaya mata kuma ita ma ta tausaya masa. Babu wanda wanda ya fi Fatima kusa da shi kuma ba wanda yake so kamar ta. Ya sha jaddada wannan alaka a cikin hadisansa yana bayyana matsayinta a cikin al'ummarsa. Ga kadan daga cikin abubuwan da ya fadi dangane da ita:
"Fatima wani yanki ne daga gare ni, wanda ya fusata ta ya fusata ni(3)". da kuma cewa:
"Lallai Fatima wani yanki ne daga gare ni, (duk) abin da ke cutar da ita yana cutar da ni (4)".A wani wajen kuma ya ce:
"Ya Fatima, ashe ba ki yarda da kasancewa shugabar matan duniya ba, kuma shugabar wannan al'umma da shugabar matan Muminai.(4)".
Fatima na girma alhali kaunar babanta gare ta na girma tare da ita, tausayinsa a kanta na karuwa; kuma ita ma tana musanya masa wannan kauna, tana cika zuciyarsa da lura; don haka ya kira ta da Ummu Abiha (wato uwa a wajen babanta)(5)"..
Ta kasance tana ji da shi da tausaya masa irin tausayin uwa ga 'ya'yanta, tana kuma lura da shi kamar yadda uwaye mata ke lura da 'ya'yansu kanana, wanda hakan ya zamanto abin koyi ne na tsarkakkar alakar uba (da 'ya'yansa) wajen gina 'ya'ya da fuskantar da dabi'u da rayuwarsu, da cika zukatansu da kauna da tausayi. Hakika wannan alaka ta zama babbar abar misali a fagen renon 'ya mace a Musulunci da lura da ita, girmama ta da daukaka matsayinta.
|
||||
| ||||
|
Allah Ya kara Maki Yarda ya 'Yar Manzon Allah (s.a.w.a.)
________________________ Ga Fatima nan tana matashiya mai cike da annuri, wadda ta tattaro daraja, kyau da daukakar matsayi, tana raye a hannun mahaifinta a Madina. Sai hankula suka fara kowama gare ta, wasu Sahabbai suka fara tunanin samun dacewar aurenta, da samun daukakar nasaba ta hanyar samun dangantaka da babanta.
Wanda dai ya fara zuwa neman auren ta shi ne halifa Abubakar, sannan sai Umar bin Khaddab, wasunsu kuma suka biyo baya. Sai dai Manzo (s.a.w.a) ya yi ta ba su uzurin rashin amsa bukatunsu da cewa: "Hukunci bai sauko ba tukuna".
Daga nan sai Ali ya yi tunanin neman auren Fatima, don haka sai ya tashi ya yi wanka sannan ya yi alwala ya kuma yafa mayafinsa ya yi nafila raka'a biyu, sannan ya sa takalmansa ya doshi Annabi (s.a.w.a) a lokacin yana dakin Ummu Salama. Ya yi sallama, Manzo ya amsa masa, sai Imam ya zauna a gaban Manzo ya dukar da kai kasa; sai Manzo ya ce masa: "Ka zo da wata bukata ne?" sai Imam ya ce: "Na'am, na zo neman auren 'yarka Fatima ne; ko za ka aurar min da ita ya Manzon Allah?" Sai Ummu Salama ta ce: "sai na ga fuskar Manzon Allah ta cika da annuri na farin ciki da murna, sannan ya kalli Ali ya yi masa murmushi. Daga nan sai Manzo (s.a.w.a) ya shiga wajen Fatima ya ce mata:
"Ali bin Abi Dalib, wannan da kika san kusancinsa da darajarsa a Musulunci, ya zo yana zance a kan al'amarinki (wato yana neman auren ki). Hakika kuwa da ma ni na roki Ubangijina da ya aurar da ke ga mafi alherin talikanSa kuma wanda Ya fi so daga cikinsu. To me kike gani?"
Sai ta yi shiru. Sai Manzo (s.a.w.a) ya fita yana cewa:
"Allahu Akbar! Shirunta yardarta ne".
Sannan ya cewa Imam Ali (a.s.):
"Ya Ali, shin kana da wani abu da zan daura maka aure da shi (sadaki)?".
Sai Imam Ali (a.s.) ya ce:
"Sai takobina da garkuwata, sai kuma rakumina na ban ruwa ", (a wata ruwayar an ce doki ne maimakon rakumin).
Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce:
"Amma takobinka kana da bukatarsa, kana yaki da shi a tafarkin Allah kuma kana kashe makiya Allah da shi. rakuminka kuma kana shayar da (gonar) dabinonka da shi, haka kana daukar kaya da shi, kuma yana daukarka a tafiye-tafiyenka. Don haka je ka yi yadda za ka yi da garkuwarka".
Sai Imam Ali (a.s.) ya je ya sayarwa Usman bin Affan da garkuwarsa a kan farashin dirhami 480, sai ya kawo wa Manzo(1) Daga nan Manzon Allah (s.a.w.a) ya sanar da Musulmi zancen auren, ya kuma cewa Ali (a.s.): "Allah Ya hore ni da in aurar maka Fatima a bisa nauyin miskali dari hudu na azurfa(2) ) in ka yarda da haka". Sai Imam ya amsa da cewa ya yarda, don haka sai Annabi ya yi masu addu'a da cewa: "Allah Ya hada kanku, kuma Ya ba ku sa'a, Ya kuma albarkace ku, Ya fitar da tsarkaka masu yawa daga gare ku". Anas bin Malik Ya kasance yana cewa: "Hakika kuwa Allah Ya fitar da tsarkaka da yawa daga gare ku (3)". Manzon Allah (s.a.w.a) ya aurar da Fatima da sadaki madaidaici, ya saya mata kayayyakin da suka yi daidai da wannan sadaki, don zamuna masu zuwa su ga cewa abin duniya fa ba kome ba ne a wajen mutuntaka da daukakar kamala. Manzo (s.a.w.a) ya karbi madaidaicin sadakin daga Ali bin Abi Dalib (a.s.), sai ya dauki nauyin shirya 'yarsa da tanajin kayan gidanta wanda ya kunshi 'yan kayayyaki kadan amma cikin daraja da daukaka. Sai ya aiki wasu Sahabbansa kasuwa don sayo mata (Fatima) abubuwan da sabon gidanta ke bukata, da suka kunshi shinfidu da lullubi da sauran bukatun gida da kayan girki tare da wasu 'yan suturu da turare(4) . Bayan wata daya (da daura aure), sai Manzo (s.a.w.a) ya fahimci bukatar Ali (a.s.) na tarewar Fatima a sabon gidanta, don haka sai ya amsa wannan bukata. Sai himmatuwa da al'amarin Fatima (a.s.) ya karu a wajen Manzo (s.a.w.a), don ya musanya mata fakuwar mahifiyar nan ta ta mai tausayi (wato Khadija), a wannan sha'ani da uwa ke da matukar muhimmanci. Don haka sai ya sa hannu da kansa a al'amarin sa Fatima a lalle. Ya nemi matansa da su shirya ta kamar yadda ake shirya 'yan mata a daren tarewa. Bayan nan sai Manzo ya hada walima da sanar da aure, Muhajirai da Ansar sun sami halartar wannan taro na farin ciki. Wannan bai zama wani sabon abu ba, himmatuwar Manzo da al'amarin Fatima bai kasance don kusanci da dangantakarsa da Ali da Fatima ba; a'a wannan bayar da muhimmanci ya samo asali ne saboda fadadar reshen Annabci da bishiyar Imamanci ta wannan iyali mai albarka. Saboda Allah Ya so aurar da zababbiyar mace kuma tsokar Annabi, Fatima, ga zababben mijinta, Ali. Don kuwa Ali (a.s.) ne wanda Manzo (s.a.w.a) dangane da shi yake cewa: "Ashe ba ka yarda ka zama a wajena irin yadda Haruna ya kasance a wajen Musa ba, in ban da cewa kawai babu Annabi a bayana ba(5)". Fatima kuwa ita ce wannan da Manzo (s.a.w.a) dangane da ita ya ke cewa: "Ashe ba ki yarda ki zama shugabar matan duniya ba". Don haka su biyun sun kasance wadanda Manzo (s.a.w.a) ya fi so daga mutane kuma wadanda suka fi kusa da shi. An taba tambayar A'isha kan mutumin da Manzon (s.a.w.a) ya fi so, sai ta amsa da cewa: "Fatima". Sai aka ce mata: daga maza fa? Sai ta ce: "mijinta, a iya sanina bai kasance ba face mai yawan salla sa azumi(6)". Haka Allah Ya so zuriyyar ManzonSa (s.a.w.a) ta fadada ta hanyar Ali da Fatima (a.s.), ya zama sun sami Hasan da Husaini, shuwagabannin samarin gidan aljanna, da sauran tsarkakan Imamai masu shiryar da wannan al'umma. Wannan babban sirri ne yasa auren Fatima (a.s.) ya kasance bisa horon Allah Madaukaki, Manzo (s.a.w.a) bai gabatar da shi ba kafin umarnin Ubangijin, bai yi wani abu ba har sai da hukuncin Allah ya sauko, kamar yadda ya tabbatar da haka da kansa. ____________ (1)- Sayyid Muhsin al-Amin, cikin al-Majalis al-Siniyyah, juzu'i na 3, shafi na 83-84. (2)- Wasu ruwayoyin sun ce sadakinta (a.s) dirhami 500 ne. (3)- Tabari, cikin Zakha'irul-Ukbah, shafi na 30 da na 31. (4)- Sayyid Muhsin al-Amin al-?mili, cikin al-Majalisil-Siniyyah, juzu'i na 2, shafi na 77-78. (5)- Tabari, cikin Zakha'irul-Ukbah, shafi na 262; Tirmizi ma ya fitar da shi; haka Ibn Abdul-Barr, cikin al-Isti'ab, juzu'i na 4, shafi na 378. (6)- Kamar na sama. |
||||||||||||||
|
